Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi da Kim sun yi musayar sakonnin murya
2020-05-09 20:23:22        cri
Sakatare Janar na JKS, kuma shugaban kasar, Xi Jinping, ya aike da sakon murya na godiya ga shugaba Kim Jong Un na Koriya ta arewa, a matsayin martani ga sakon muryar da shugaban Kim din ya aike masa da shi tun da farko.

Xi Jinping ya bayyana cewa, bayan barkewar COVID-19, kasar Sin, karkashin shugabancin kwamitin tsakiya na JKS da goyon bayan daga bangarori daban daban, ta cimma gagarumin sakamako wajen karewa da dakile yaduwar COVID-19 ta hanyar tsauraran matakai.

Shugaba Xi ya kara da cewa, a shirye Sin ta ke ta fadada hadin gwiwar yaki da annobar da Koriya ta arewa, tare da taimaka mata da bukatunta iya karfinta.

Tun da farko a sakon murya da ya aikewa shugaba Xi a ranar Alhamis, shugaba Kim ya yaba masa tare da taya shi murnar jagorantar JKS da al'ummar Sinawa, wajen cimma dimbin nasarori a yaki da annobar.

Ya ce ya yi ammana, karkashin shugaba Xi, JKS da al'ummar Sinawa za su kara fadada sakamakon da suka samu don cimma nasara ta karshe mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China