Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci hadin gwiwar kasa da kasa don yaki da COVID-19
2020-05-08 11:01:11        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci kasashen duniya su kawar da duk wani nuna banbanci kana su nuna goyon baya ga juna, sannan a yi watsi da duk wasu zarge-zarge marasa tushe, a bada fifiko wajen yin hadin gwiwa domin yaki da annobar COVID-19.

Ya yi wannan tsokaci ne a tattaunawar da ya yi ta wayar tarho tare da takwaransa na kasar Uzbekistan, Shavkat Mirziyoyev.

A madadin gwamnatin Sin da al'ummar Sinawa, Xi ya mika sakon jajantawa da kuma nuna goyon baya ga takwarorinsu al'ummar Uzbekistan game da yakin da suke yi da annobar COVID-19.

Xi ya ce, annobar COVID-19 tana kara tabbatarwa duniya cewa, gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama ita ce hanya mafi dacewa, ya kara da cewa, nuna goyon baya ga juna da yin hadin gwiwa su ne muhimman makaman yaki da annobar, wacce ta kasance abokiyar gaban dukkan bil adama da kawo koma baya ga ci gaba da makomar duniya baki daya.

A nasa bangaren, Mirziyoyev ya ce, karkashin shugaban Xi mai cike da hikimomi, gwamnatin Sin ta dauki kwararan matakai, kuma masu inganci inda kasar ta samu nasarar dakile annobar a cikin kankanin lokaci. Ya godewa gwamnatin kasar Sin da al'ummarta sakamakon samar da tallafin kayayyakin jin kan bil adama ga kasar Uzbekistan a lokacin da take halin fama da wahalhalu, kana ya kara godewa kasar Sin bisa ga musayar kwarewa da kuma taimakon da take baiwa kasarsa, ya ce kasar Uzbekistan ta samu gagarumin ci gaba a aikin kandagarki da dakile annobar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China