Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: An samar da kowace kasa dukkan bayanai game da COVID-19 tun farkon barkewar cutar
2020-04-21 10:17:14        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO a takaice, ta bayyana a jiya Litinin cewa, ta yi aiki kafada da kafada da masana daga kasar Amurka, musamman bayan barkewar COVID-19, kuma tun lokacin da cutar ta barke, ba ta boye komai game da cutar ga sauran kasashe ba.

Babban darektan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi a taron da hukumar ta shiya ta kafar bidiyo daga Geneva. Ya ce, hukumarsa da cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Amurka(CDC), sun dade suna hadin gwiwa, kuma babu wani abin da aka boyewa hukumar game da wannan annoba.

Tun farko dai, jaridar Washington Post ta ba da rahoton cewa, masanan Amurka dake aiki da hukumar WHO, suna sanar da fadar Amurka ta White House abubuwan dake faruwa, yayin da cutar ta barke a kasar Sin a karshen shekarar 2019.

Sabanin zargin da shugaba Donald Trump na Amurka ya yi cewa, WHO ta boye bayanai game da barkewar cutar, jaridar ta nuna cewa, manyan jami'an lafiya na kasar Amurka sun yi ta ganawa akai-akai da takwarorinsu na WHO.

Jami'in na WHO ya ce, "Mun yi ta yin gargadi, mun yi ta yin gargadi tun lokacin da aka samu rahoton bullar cutar. Wannan abokiyar gaba ce da kowa zai yaka, muna bukatar hadin kai, da sadaukar da kai daga kasashen duniya don ganin bayan wannan annoba.". (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China