![]() |
|
2020-04-28 10:20:50 cri |
Tedros Ghebreyesus ya ce, WHO na ci gaba da damuwa game da yadda adadin masu kamuwa da cutar ke karuwa a nahiyar Afrika da gabashin Turai da Latin Amurka da wasu kasashen Asiya.
Ya bayyana yayin wani taron manema labarai ta kafar bidiyo daga Geneva cewa, akwai kasashe a dukkan wadancan nahiyoyi da ba sa iya gabatar da ainihin alkaluman wadanda suka kamu ko suka mutu sanadin cutar, saboda rashin karfin gwaji.
Ya kuma bayyana cewa, WHO na ci gaba da ba wadancan kasashe taimakon da ya kamata, yana mai cewa, cikin mako guda da ya gabata, an kai kayayyaki zuwa sama da kasashe 40 na nahiyar Afrika.
Ya kuma kara da cewa, cikin makonni masu zuwa, za a kara tura miliyoyin kayayyakin, inda ya ce ana shiri sosai. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China