Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin likitancin Sin: babu hujja a ce wai "cutar COVID-19 ta yi yoyo daga dakin gwaje-gwaje na Wuhan"
2020-05-08 20:05:02        cri
Game da jita-jitar da wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suke ta kara yadawa, cewa wai "cutar COVID-19 ta yi yoyo daga dakin yin gwaje-gwajen cututtuka na Wuhan", masani a fannin likitanci Cai Shenghe, wanda ya samu digiri na biyu a dakin gwaje-gwajen na Wuhan, kuma ya kammala karatun gaba da digiri na uku a kwalejin likitanci na jami'ar Harvard Medical School, a kwanan baya ya zantawa da manema labarun CMG, inda ya bayyana cewa, babu wasu shaidu game da wancan zargi, kuma maganar ta sabawa babban tushen kimiyya. Ya kara da cewa, dole ne a warware matsalar asalin kwayar cutar tare da hujja, kuma bisa manufar kimiyya.

Cai ya nuna cewa, babu alamar dake nuna cewa, an harhada cutar bisa taimakon dan Adam. Ya ce, ba a dakin gwaje-gwajen cututtuka na Wuhan ne asalin cutar ba. Ya kuma yi tsokaci da cewa, idan an ce cutar ta yi yoyo ne daga dakin dwaje-gwaje na Wuhan, to ko shakka babu wadanda za su kamu da cutar a farko su ne mutanen dake a wurin, wadanda ke mu'amala da cutar. Ke nan kamata ya yi a samu yaduwar annobar daga dakin. A irin wannan yanayi na rashin kayayyakin kiyaye lafiya, ya kamata a ce an samu akalla mutane fiye da goma da aka tabbatar sun kamu da cutar, wasu daga cikinsu kuma sun mutu, yayin da wasu fiye da dari daya za su harbu da cutar. Amma, a hakika dai a cikin ma'aikata da dalibai sama da 100 dake dakin nan, babu wanda ya kamu da cutar. Hakan ya tabbatar da cewa, cutar COVID-19 ba ta yi yoyo daga dakin gwaje-gwajen cututtuka na Wuhan ba.(Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China