Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta riga ta turawa kasashe 16 tawagogin masanan jiyya don yakar COVID-19
2020-05-02 20:48:30        cri

Yau Asabar, mai magana da yawun ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin kana mataimakin babban direktan ofishin fadakarwa ta kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin Mi Feng, ya shedawa manema labarai cewa, bisa sanarwar da WHO ta bayar, an ce, cutar COVID-19 tana yaduwa a kasashe da kuma yankuna 213, kana karin mutanen dake kamuwa da cutar a ko wace rana ya haura dubu 60 a cikin ranaku 30 a jere da suka gabata. Ya kara da cewa, Sin ta riga ta tura tawagogin masanan jiyya har sau 15 dake kunshe da masanan jiyya 149 zuwa kasashe 16. Ya zuwa yanzu, hukumar tsaron kasar Serbia ta baiwa tawagar kasar Sin lambar yabo ta matsayin koli wajen kare kasar. Mi Feng ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da sauran kasashe don yakar cutar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China