Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Richard Horton: Bai kamata a baza jita-jita kan COVID 19 ba
2020-05-02 16:04:56        cri

Babban editan Mujallar "The Lancet" Richard Horton ya zanta da manemi labaru na kafar CMG a jiya Juma'a, inda ya bayyana ra'ayinsa game da jita-jitar da ake yi kan cutar COVID 19.

Game da jita-jitar dake cewa, cutar ta samo asali daga kasar Sin, Richard Horton ya ce, wadannan maganganu sun ba shi dariya matuka, amma duk da haka akwai bukatar a mai da hankali kan su. Ya ce jita-jita ba za su taimaka wajen tinkarar cutar ba ko kadan, yana mai cewa, ya kamata a yi bincike da nazarin asalin kwayar cutar bisa kimiyya. Ya yi gargadin kada wadannan abubuwa su illata tunanin jama'a, domin za su kawo babbar barazana ga duniya baki daya.

A cewarsa, yana takaicin wasu 'yan siyasar Amurka, saboda ganin yadda suke baza jita-jita da goyon bayan wasu shirye-shiryen jiyya da ba su da sahihanci, tare da sukar sauran kasashe ko kungiyoyi. A ganinsa, wadannan matakai ba su da wani amfani ko kada. Richard Horton yana mai cewa, ya kamata a kara hadin kai don tinkarar kalubale masu dimbin yawa da cutar ke haddasawa a fadin duniya. Ya ce, kawo baraka tsakanin kasashe da jama'arsu zai rage karfin bil Adama na yakar wannan mummunar cuta dake dabaibaye duniya.

Ya ce hanyar da ta dace a bi ita ce, kwatantar da hankalinmu da kuma neman yin hadin kai da gwamnatin kasar Sin wajen fahimtar cutar, ta yadda za a iya yin iyakacin kokarin tabbatar da magance cutar ta sake kunno kai a duniya nan gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China