Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin kandagarkin COVID-19 na majalisar gudanarwar Sin ya kira taron manema labarai
2020-05-08 16:28:01        cri

Da safiyar yau Juma'a misalin karfe 10, kwamitin hadin gwiwa na kandagarkin COVID-19 na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira wani taron manema labarai, inda mataimakin ministan ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Sin Liu Xiaoming ya nuna cewa, daga ranar 1 zuwa 5 ga wata, yawan fasinja da aka jigila ta hanyar jirgin kasa da motoci da kuma jirgin ruwa da na sama ya kai miliyan 121.

Mataimakin darektan hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Li Bin ya nuna cewa, lokacin hutu na ranar ma'aikata ta kasa da kasa, ba a samu mutanen da suka kamu da cutar da ba a san asali ba, ko a cikin taron jama'a.

Ban da wannan kuma, mamban hukumar JKS ta ma'aikatar al'adu da yawon shakatawa Wang Xiaofeng ya ce, a wannan lokaci yawan masu bude ido a cikin kasar ya kai miliyan 115, kana yawan kudin shigar da aka samu a wannan fanni ya kai RMB Yuan biliyan 47.56.

Mataimakin ministan ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Wang Bingnan ya ce, alkaluman da aka bayar a wannan lokaci ya nuna cewa, kasuwanni a cikin gida na samun farfadowa, kuma yawan kudin da aka kashe ya karu da kashi 32.1% bisa na bikin share kaburbura na gargajiyar kasar a watan Afrilu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China