Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin: sama da kaso 80% na kamfanonin samar da hidimomin rayuwa na kasar sun koma bakin aiki
2020-05-03 17:05:06        cri

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana kwanan nan cewa, a yayin da ake ta samun sassaucin yanayin cutar COVID-19 a kasar, sama da kaso 80% na kamfanonin samar da hidimomin rayuwa na kasar sun koma bakin aiki.

Kakakin ma'aikatar, Mr. Gao Feng ya bayyana cewa, har yanzu akwai wasu kamfanonin dake fuskantar matsalar karancin masu sayen kayayyakinsu da karancin kudin shiga. Ma'aikatar za ta hada kan sassan da abin ya shafa, don tsara manufofi na tallafawa kananan kamfanoni da ma kamfanoni masu zaman kansu, don sassauta kudin da suke biya wajen hayar ofisoshi. Ban da wannan kuma, ma'aikatar za ta aiwatar da gwajin samar da hidimar rayuwa a wasu unguwanni, don sa kaimi ga mazauna unguwanni wajen sayen kayayyaki. Sannan kuma, za ta aiwatar da shirin farfado da gidajen cin abinci, ta yadda za su bunkasa yadda ya kamata.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China