Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Budaddiyar wasika ga Trump daga wata nas da ta dawo daga asibitin Wuhan
2020-05-08 16:33:40        cri

Mai martaba shugaba Donald Trump:

Ni wata nas ce a sashin kula da numfashi, na je birnin Wuhan, wurin da cutar ta fi kamari, kuma yanzu na dawo garinmu. Ba zan manta da aikin da mu masu aikin jiyya dubu 42 muka yi a Wuhan, ba dare ba rana ba. Yanzu, ina son in rubuta maka wannan wasika don bayyana labarin Wuhan.

Lokacin da na tashi zuwa Wuhan, biki ne na sabuwar shekara ta kasar Sin bisa kalandar gargajiya ta kasar, kamar jajibirin ranar kirismeti a Amurka, wannan lokaci na da muhimmanci sosia ga iyalai, amma masu aikin jiyya muna da nauyin ceton mutane.

Wannan cuta ta zo cikin gaggawa. Da farko, muna karancin kayayyakin jiyya matuka, domin yin tsimin wadannan kayayyaki, ba ma cire rigar kandagarki, duk da cewa akwai matukar zafi. Hakan ya sa, da na ga masu aikin jiyya na Amurka sun sa leda don kandagarki, na fahimci halin da suke ciki. Kuma ina bakin ciki matuka da ganin masu aikin jiyya rike da hotunan iyalansu wadanda suka rasu sakamakon cutar.

Amma, abin da ya faranta min rai shi ne, mutane da dama sun sami sauki sun bar asibiti, musamman ma tsoffi. Tsoffin dubu 3 da dari 6 da shekarunsu ke sama da 80 a lardin Hubei sun warke daga cutar, sakamakon jiyyarsu da muka yi. Ina farin ciki matuka, kuma da alfahari, saboda wadannan tsoffi sun taba yin iyakacin kokarin raya kasarmu, yanzu muna da damar ceton rayukansu da iyakacin kokarinmu.

A birnin Wuhan, daga tsoho dake da shekaru 108 a duniya zuwa jaririn da aka haifar sa'o'i 30, muna yin iyakacin kokarin ceton su. Saboda ceton mutane da jinyarsu aikinmu ne. Rayukan mutane na da matukar muhimmanci a nan kasar Sin.

Mai martaba shugaba, duk wadannan su ne al'amuran da suka faru a Wuhan.

Na sani, a wannan lokaci, jama'ar Amurka na fama da wannan mumunar cuta sosai, masu jiyya a kasar suna kokarin gudanar da aikinsu, kuma wasu na ba da taimako ga wasu. Ina mutunta wadannan mutane sosai. Sannan kuma, ina fatan alheri ga jama'ar Amurka.

Wasika daga wata nas da ta dawo daga asibitin Wuhan

4/5/2020

(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China