Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Amurka ta karbi binciken da kasa da kasa su yi kan batun yaduwar cutar COVID-19 a kasar
2020-05-05 17:03:50        cri

A kwanakin baya, wasu 'yan siyasar kasar Amurka ciki har da Mike Pompeo sun raina yanayin yaduwar cutar COVID-19 a kasar Amurka, da ci gaba da yada jita-jita wai cutar ta bulla daga cibiyar nazarin kwayoyin cuta ta Wuhan ta kasar Sin, kana sun ce ya kamata kasa da kasa su yi bincike kan cibiyar. Wannan yunkurinsu ne na kaucewa kuskurensu don dorawa wasu laifi. A hakika dai, kafofin watsa labaru na kasa da kasa ciki har da manyan kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun yi tsammani cewa, ya kamata kasa da kasa su yi bincike kan kasar Amurka, wadda take da alakar yaduwar cutar a kasar, har ma duk duniya.

 

 

Da farko dai, ya kamata kasar Amurka ta amince hukumomin kasa da kasa kamar WHO su shiga dakin gwaji na Fort Detrick na kasar da yin bincike don amsa bukatu da matsalolin da jama'ar kasar suke da su. Na biyu, ya kamata kasar Amurka ta hada gwiwa da hukumomin kasa da kasa da binciken ko an yi amfani da yanayin yaduwar cutar mura don boye hakikanin yanayin yaduwar COVID-19 a kasar. Na uku kuma, ya kamata kasar Amurka ya yi hadin gwiwa da kasa da kasa don binciken lokaci na farko da cutar COVID-19 ta bulla a kasar.

 

 

Game da binciken da kasa da kasa suka yi, kasar Sin ta nuna sahihanci da kuma bude kofa ga kasa da kasa. Amma kasar Sin ta ki amincewa da yin amfani da binciken kasa da kasa don cimma yunkurin siyasa, da zarginta da yada jita-jita ba tare da tushe ba. Cutar ta bulla a wurare da dama a duniya, kana ba a san asalinta ba, ya kamata a yi bincike cikin adalci, da daidaito ga kasashen da abin ya shafa, ta hakan za a gano asalin cutar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China