Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zuwa yaushe ne 'yan siyasar Amurka za su bayyana ainihin yanayin cutar da kasarsu ke ciki?
2020-05-06 22:00:15        cri

"Na yi zaton ko na kamu da cutar COVID-19, amma sun ce an fara gano bullar cutar a kasar Amurka a watan Janairu. A baya na taba kamuwa da cutar mura, sai dai ba ta kai tsananin haka ba, har ma na ji tamkar zan mutu." Kwanan nan, furucin da magajin garin birnin Belleville a jihar New Jersey, Michael Melham ya yi, ya jawo hankalin kasa da kasa. Inda ya ce yana zaton ya kamu da cutar a watan Nuwambar bara, kuma sakamakon gwajin da aka yi masa ma ya shaida cewa, yana dauke da kwayoyin halittar dake kare kansa daga harbuwa da wannan cuta.

Hakika, kafin wannan furuci na Michael Melham, tuni shugaban cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta Amurka Robert Redfield ya bayyana a fili cewa, wasu da suka mutu a yayin yaduwar cutar mura a watan Satumbar bara, a hakika cutar COVID-19 ce ta kama su. Abun tambaya a nan shi ne, mutane nawa ne aka yi zaton sun kamu da cutar? Kuma a hakika sun mutu ne sakamakon cutar COVID-19. Ko tun a watan Satumbar bara ne cutar COVID-19 ta fara yaduwa a tsakanin unguwannin kasar?.

Baya ga haka, a karshen watan Faburairu, fadar White Housa ta nemi jami'an kasar, da sassan lafiya, da ma masanan da abin ya shafa, da su samu amincewa daga ofishin mataimakin shugaban kasar kafin su yi wani furuci a fili game da annobar. Sai kuma ya zuwa ranar 2 ga watan Maris, cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar ta daina samar da alkaluman da suka shafi mutanen da aka yi wa gwaji, da kuma wadanda suka mutu sakamakon cutar, bisa dalili na wai alkaluman ba su yi daidai ba. A sakamakon gazawar gwamnati kuma, har yanzu wata jami'ar kasar ce ke kula da aikin kididdigar.

'Yan siyasar Washington sun yi ta boye yanayin cutar da kasar ke ciki, tare da lalata kokarin da ake yi na yaki da cutar, don neman boye gazawarsu wajen gudanar da harkokin mulki. Hakan kuma ya bayyana dalilin da ya sa cutar ke ta yaduwa a kasar dake kan gaba a duniya ta fannin kiwon lafiya da fasahohin kimiyya.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China