Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump: NBC Da CNN Su Ne 'Yan Koran Sin, Abokan Gaban Jama'ar Amurka
2020-05-05 13:02:32        cri
A ranar 1 ga wata, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi zargi a shafinsa na Twitter cewa, kamfanin watsa labaran a duk fadin kasar Amurka na NBC da kamfanin dillancin labarai na CNN su ne 'yan koran kasar Sin, kana abokan gaban al'ummar kasar Amurka. Wannan shi ne sabon zargin da shugaba Donald Trump ya yi wa manyan kafofin watsa labaran kasarsa, bayan zargin da ya yi wa gidan rediyon VOA cewar, yana taimakawa kasar Sin a fannin fadakar da jama'a.

Donald Trump ya yi wannan zargi ne sabo da wadannan labaran da aka fidda.

A watan Maris, kamfanin dillancin labarai na CNN ya fidda labarai cewa, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Italiya, kasar Sin ta aika tawagar likitoci zuwa kasar, ta da samar wa kasar Italiya kayayyakin jinya da take bukata, kuma. Kamfanin ya ce, a halin yanzu, manufar "Amurka da Farko" da Donald Trump ya fidda, kusan ba ta da amfani, shi ya sa, "kasashen Turai ba su da damar yin zabi".

Sa'an nan, a ranar 14 ga watan Afrilu, dan jaridar CNN Jim Acosta ya bayyana cewa, Donald Trump yana son dauke hankulan al'umma daga abubuwa dake faruwa, kuma kasar Sin da gwamnatin Barack Obama da kafofin watsa labarai da hukumar WHO dukkansu, su zama "masu daukar alhakin laifukan Donald Trump", sabo da Donald Trump yana zargin kowa da kowa, amma ban da kansa.

A ranar 29 ga watan Afrilu kuma, CNN ya fidda wani sharhi, inda ya kwatanta yadda kasar Sin da kasashen yammacin duniya suke tunkarar cutar numfashi ta COVID-19. Ya ce, ta fuskar dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin ta riga sauran kasashen duniya daukar matakai yadda ya kamata, ko da yake, wadannan kasashe suna da karin lokaci da damammaki wajen hana yaduwar cutar.

Bugu da kari, babban gidan rediyon VOA ya taba fidda labarin cewa, matakan da birnin Wuhan na kasar Sin ya dauka sun zama abin koyi ga duniya, ya kuma yi bayani kan kididdigar da kasar Sin ta yi kan annobar, domin kwatanta adadin rasuwar mutane sakamakon cutar a kasar Sin da kuma a kasar Amurka. Lamarin da ya zama abun zargi a wajen gwamnatin kasar Amurka, inda ta ce, Gidan rediyon VOA ya kashe kudaden al'ummomin kasar Amurka, amma bai "yada labaran kasar Amurka yadda ya kamata" ba, har ma yana taimakawa abokiyar gabar Amurka wajen fadakar da jama'a.

Dukkanin labaran nuna amincewa kan kasar Sin da kafofin watsa labaran kasar Amurka suka fidda, ba yabo ne ga kasar Sin ba, ainihin abubuwan da suka faru a kasar Sin ne. Kuma kwatanta yadda kasar Sin da kasar Amurka suke fuskantar cutar numfashi ta COVID-19, ya matsa wa gwamnatin Donald Trump lamba, wannan shi ne dalilin da ya sa, ya yi wannan zargi. (Mai Fassarawa: Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China