Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin bata sunan kasar Sin, da siyasantar da yanayin da duniya ke ciki, ba za su goge gazawar Amurka na kare al'ummarta ba
2020-05-05 17:40:38        cri
Kawo yanzu, duniya na cikin wani matsanancin yanayi da ba a taba gani ba a tarihi. Dan Adam na fuskantar kalubalen da yawa daga cikin al'ummar duniya masu jini a jika, ba su taba gani ba. Barkewar cutar COVID-19 a karshen bara, ya jefa al'ummomin duniya cikin tasku da tashin hankali. Sai dai a dadidai wannan lokaci da ya kamata tsare rayuka da lafiyar al'umma su zama abubuwan da aka fi ba muhimmanci, wasu na amfani da wannan yanayi wajen siyasantarwa da yin wasarairai da rayukan jama'a. Cuta ba ta san iyakar kasa ko launin fata ko addini ba. Maimakon barkewar wannan cuta ta zama dama ta hadin kai da nunawa duniya cewa mokama daya dukkan bil adama suke da shi, abun takaici, sai ake amfani da ita wajen karkatar da hankalin jama'a da siyasantar da rayukansu.

Har yanzu batun asalin cutar COVID -19 na ci gaba da zama abun da wasu kasashen yamma ke ba muhimmanci fiye da tsaron rayukan al'ummarsu. Neman gano asalin cutar abu ne mai ma'ana, sai dai hanyar da aka dauko, sam ba ta dace ba, kuma ba mai bullewa ba ce, don maimakon hada kan duniya, nema take ta kawu rarrabuwar kawuna da nuna yatsa da kuma wariya tsakanin bil adama.

A baya-bayan nan, yayin zantawa da kafar yada labarai ta NBC ta Amurka, sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya bayyana cewa, kasarsa ta samu shaidun dake cewa kirkiro kwayar cutar Corona aka yi a wani dakin gwaji dake birnin Wuhan na kasar Sin. Sai dai yayin jawabin nasa, ya gaza gabatar da shaidar da ta tabbatar da wannan furuci. Ya kuma kara da cewa, ba za su gaji da neman asalin cutar ba, domin suna da kwararrun da za su gano gaskiya. Ke nan ashe ba su kai ga tantance gaskiyar batun ba, amma ya yi riga mallam masallaci, ya furuta cewa kirkiro cutar aka yi a kasar Sin. Irin wadannan zantuttuka daga bakin babban jami'in gwamnatin babbar kasa a duniya, sam bai dace ba. Wannan tamkar zubar da kima ne da rashin sanin ya kamata.

A makon da ya gabata, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng ya zanta da kafar watsa labarai ta NBC, inda ya bayyana cewa, kasar Sin na gudanar da harkokinta a bayyane kuma bisa gaskiya, kuma tana goyon bayan musayar bayanai tsakanin masanan kimiyya. Wannan na nufin babu wani abu da kasar Sin take boyewa, kuma tana goyon bayan binciken masana, bisa dabarun kimiyya da fasaha, amma ba neman bata mata suna ta hanyar shafa mata bakin fenti bisa zargin da ba shi da tushe ba.

Idan za a iya tunawa, kasar Sin ba ta tsaya jan kafa ba wajen sanar da hukumar WHO da sauran kasashen duniya, ciki har da Amurka, a lokacin da ta tabbatar da bullar cutar. Wanda ya zama mataki da har yanzu kasashen duniya ke jinjina mata akai. Baya ga sanar da su da ta yi, ta ci gaba da fitar da bayanai daki-daki game da yanayin cutar, da adadin wadanda suka kamu, da wadanda suka mutu, da kuma jinyar wadanda suka kamu. Wadanda duka suka taimaka wajen ba kasashen duniya dabarun kandagarkin cutar.

Har ila yau, kasar Sin ta gayyaci kwararru daga WHO da kasa da kasa inda suka zo suka yi nazarin yanayin cutar. Shin idan tana da hannu wajen kirkirar cutar, za ta dauki dukkan wadannan matakai? Kasar Sin kasa ce dake sanya tsaro da lafiya da dukkan muradun al'ummarta sama da komai. Don haka, me zai kai ta ga kirkiro cutar da za ta hallaka al'ummarta da gurgunta harkokin tattalin arziki da kuma zamantakewarsu? Wannan cuta ta kama Sinawa sama da dubu 84, haka kuma ta hallaka sama da dubu 4, baya ga makudan kudi da aka zuba wajen yaki da ita a kasar Sin, lamarin da ya kai tattalin arzikinta ga sauka karon farko cikin gomman shekaru.

Gazawar Amurka wajen daukar matakan kandagarki da sauran dabarun tunkarar cutar, har ta yi mata mugun kamu, bai zama abun dogaro wajen neman dorawa kasar Sin laifi ba. Bisa la'akari da bayanan da kasar Sin ta yi ta samarwa, to idan Amurka ba ta gode mata ba, Sin ba ta cancanci zagi ba. Kamata ya yi a kyale masana kimiyya su yi aikinsu. Ban da haka ma, WHO da sauran masu ruwa da tsaki, sun sha jadadda cewa, kwayar cutar ba ta halayya irin ta wadda ake kirkira a dakin gwaji. Amma 'yan siyasar Amurka, sun nace suna son bata sunan kasar Sin bisa wani dalili nasu, abun da ba su fahimta ba shi ne, yunkurin nasu kara illa zai yi ga gazawarsu na daukar matakai da dabarun da suka kamata na kare rayuka da lafiyar al'umma.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China