Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta kaddamar da shirin taimakawa kasashe marasa karfi wajen yaki da COVID-19
2020-05-08 10:04:20        cri
A jiya ne MDD ta kaddamar da shirin agajin jin kai, da zai bukaci tsabar kudi dala biliyan 6.69, don taimakawa kasashe masu rauni jure tasirin annobar COVID-19.

A ranar 25 ga watan Maris ne dai, aka kaddamar da shirin agajin,wanda da farko ake bukatar dala bilkiyan biyu. Sai dai bayan yi masa kwaskwarima, sabon shirin ya sanya karin kasashe guda 9, da suka hada da Benin, da Djibouti, da Liberiya, da Mozambique, da Pakistan. Sauran sun hada da Philippines, da Saliyo, da Togo da kuma kasar Zimbabwe. Abin da ya kawo jimillar kasashe 63.

Da yake karin haske yayin kaddamar da sabon shirin ta kafar bidiyo, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai, Mark Lowcock, ya ce, akwai bukatar daukar matakan gaggawa, don taimakawa kasashe masu karamin karfi.

Ya ce, yanzu haka, annobar COVID-19 ta shafi kusan dukkan kasashen duniya, dama kowa ne mutum dake duniyar nan. Amma, kasashe matalauta ne za su fi dandana mummunan tasirin wannan annoba. Don haka, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa sabon shirin.

Baya ga tasirin da annobar ta yiwa sashen lafiya kai tsaye, koma bayan tattalin arziki da matakan da kasashe suka dauka don hana yaduwar cutar, su ma za su yi mummunan tasiri kan kasashe matalauta.

Don haka, ya yi gargadin cewa, akwai yiwuwar a cikin watanni uku zuwa shida masu zauwa, cutar za ta kai kololuwarta a galibin kasashe matalauta. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China