Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD da abokan huldarta, na tallafawa kasashen Burkina Faso da Mali da Niger dake fama da rikici, wajen yaki da COVID-19
2020-05-05 10:25:39        cri
MDD da hukumomin agaji, na tallafawa 'yan gudun hijira miliyan 1.2 da masu neman mafaka 107,000, dake yankunan iyakar tsakiyar yankin Sahel mai fama da rikici da annobar COVID-19.

Kakakin sakatare Janar na MDD, Stephane Dujarric, ya ce baya ga wadancan mutane, akwai wasu sama da miliyan 3 dake cikin tsananin bukatar abinci, kana adadin wadanda suka rasa matsugunansu a inda iyakokin kasashen Burkina Faso da Mali da Niger suka hadu, ya ninka har sau 4, a kan na bara.

Ya ce zuwa karshen watan Afrilu, kaso 12 cikin 100 na dala miliyan 988 da ake bukata na agajin jin kai kadai majalisar ta karba.

Tun daga farkon bana, asusun agajin jin kai na majalisar, ya ware dala miliyan 42 ga kasashen yankin tsakiyar Sahel, domin samar da abinci, da sinadaran gina jiki, da ruwa, da kayayyakin tsaftar muhalli da jiki, da na kariya da kiwon lafiya, da kuma da matsuguni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China