Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya taro kan hadin gwiwar Sin da Nijeriya a Abuja
2019-05-17 11:06:21        cri
Jiya Alhamis an shirya wani taro mai taken "cimma ra'ayi daya tsakanin Abuja da Beijing", ko kuma Abuja-Beijing Consensus a Turance a Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya, wanda kamfanin jaridar Leadership ta Nijeriya ya shirya.

Zhou Pingjian, jakadan kasar Sin a Nijeriya ya bayyana a yayin taron cewa, kasar Sin tana son inganta tuntuba da cudanya da Nijeriya, da zurfafa dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasashen 2 da kyautata hadin gwiwarsu ta fuskar tsaro, da kara azama kan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", a kokarin kara kawo wa kasashen 2 da jama'arsu alheri na a-zo-a-gani.

Mahalarta taron 'yan Nijeriya, sun yi kira ga gwamnatin kasar da ma bangarori daban daban na kasar, da su yi koyi da kyawawan fasahohin kasar Sin wajen farfado da kasa da fitar da jama'a daga talauci. Suna ganin cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya", ba shawarar yin hadin gwiwa ba ne kadai ga Nijeriya, domin za ta sabunta huldar abota a tsakaninta da sauran kasashe. Sun ce kamata ya yi Nijeriya ta bude kofarta ga shawarar ba tare da wata rufa-rufa ba, ta kuma yi amfani da damar da shawarar za ta kawo mata domin gaggauta raya kanta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China