Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi ya gana da shugaban kasar Nijeriya
2019-09-06 09:23:53        cri
A jiya ne, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma direktan ofishin harkokin waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Yang Jiechi ya gana da shugaban kasar Nijeriya Muhammad Buhari a birnin Abuja, fadar mulkin kasar Nijeriya.

A yayin ganawar, Yang Jiechi ya bayyana cewa, akwai kyakkyawar makoma kan bunkasuwar kasashen Sin da Nijeriya. Ya kamata Sin da Nijeriya su kara yin mu'amala a tsakanin manyan jami'ansu, da inganta hadin gwiwarsu a harkokin kasa da kasa da yankuna. Ya ce, an samu nasarori a hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, wadanda suka amfanawa kasashen biyu da jama'arsu. Sin ta bukaci karin kamfanonin kasar da su zuba jari a kasar Nijeriya. Yang ya kara da cewa, ya kamata a ci gaba da yin kokarin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da aiwatar da ayyukan da aka cimma a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka don zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Nijeriya.

A nasa bangare, shugaba Buhari ya bayyana cewa, kasarsa tana maraba da karin kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar. Ya ce, Nijeriya ta nuna yabo ga shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma tana fatan hada kai tare da kasar Sin wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a gun taron kolin Beijing na FOCAC, ta yadda za a inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China