Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata Sin da Amurka su yi yaki da annobar COVID-19 cikin hadin gwiwa
2020-04-30 13:32:32        cri
Le Yucheng, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya ce, a wannan muhimmin lokacin da ake yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su ajiye sabani da rikici a gefe guda, su yi yaki da abokiyar gaba wato annobar COVID-19 cikin hadin gwiwa, a maimakon sukar juna, da wasan siyasa.

A yayin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon NBC na Amurka a ranar 28 ga wata, Le Yucheng ya nuna cewa, kasar Sin, ita ce wadda annobar ta shafa, amma ba kawar annobar ba. Ya ce neman kasar Sin ta dauki alhakin yaduwar annobar da kuma neman diyya daga wajenta, wasan siyasa ne maras ma'ana. Da farko dai babu shari'a ko kuma doka a duniya, wadda ta ce, dole ne kasar da ta zama ta farko da ta gabatar da rahoton barkewar annoba ta dauki alhakinta, yana mai cewa ba a taba yin haka ba a tarihin dan Adam. Sa'an nan kuma, kasar Sin ta zama kasa ta farko da annobar COVID-19 ta shafa, ta sadaukar da dukiyoyi da rayuka da yawa don hana yaduwar annobar, ta dakatar da yaduwar annobar zuwa sauran sassan duniya, ta kuma tattara kyawawan dabarun yaki da annobar, don haka, ta ba da nata babbar gudummowa. Kamata ya yi a yi wa kasar Sin adalci, a maimakon sukarta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China