Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da bincike mara tushe saboda neman dora alhaki
2020-04-30 11:41:10        cri
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng, ya ce kasarsa na adawa da abun da ya kira bincike daga kasashen waje domin neman dora alhaki, dangane da asalin kwayar cutar COVID-19.

Le Yucheng ya bayyana haka ne yayin zantawa da kafar yada labarai ta Amurka a ranar Talata.

Ya ce kasar Sin na gudanar da harkokinta a bayyane kuma bisa gaskiya, kuma tana goyon bayan masayar bayanai tsakanin kwararrun kimiyya, ciki har da musayar nazarin yanayin da ake fuskanta.

Amma a cewarsa, abun da take adawa da shi, shi ne, tuhuma ba tare da hujja ba, yana mai cewa, bai kamata a fara da zargin kasar ba, sannan kuma a gudanar da bincike kawai saboda a kirkiro hujja. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China