Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci masu yawon bude ido su kasance masu lura da matakan dakile cutar COVID-19 yayin hutun kasa dake tafe
2020-04-30 20:48:40        cri

Mahukuntan kasar Sin sun yi kira ga al'ummar kasar, da su kasance masu sanya ido, kan dukkanin wani yanayi da ka iya haifar da yaduwar cutar COVID-19, yayin da suke tafiye-tafiye, lokacin hutun kwanaki 5 na ranar ma'aikata dake tafe.

Ministan ma'aikatar raya al'adu da yawon shakatawa na kasar Luo Shugang, shi ne ya bayyana wannan umarni, yayin wani taron manema labarai da ya gudana yau Alhamis a nan birnin Beijing. Ya ce ana kira ga masu yawon bude ido, da su nemi masaukai kafin lokacin da za su isa wuraren ziyara, su kuma gabatar da rahoton lafiya na gaskiya a duk lokacin da aka bukaci hakan. Kaza lika su ba da damar a gwada zafin jikin su, tare da kaucewa gwamutsuwa da juna. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China