Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo Yana Takalar Duniya
2020-04-30 21:01:00        cri

A jiya Laraba, sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Mike Pompeo, ya sake zargin hukumar lafiya ta duniya WHO da "shan kaye" a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19, inda ya yi barazanar gudanar da bincike kan hukumar, domin wai "ba ta yi amfani da kudin da Amurkawa suka ba ta yadda ya kamata ba".

Hakika a wannan lokacin da yanayin yaduwar cutar ke kara tsanantawa a kasar Amurka, mista Pompeo na ci gaba da kokarin dora wa sauran bangarori laifi, maimakon dukufa wajen ceton rayukan jama'ar kasarsa. Ma iya cewa, yana kokarin takalar mutanen duniya ne a wannan karo.

Sabanin maganar Mike Pompeo, ainihin wandanda suka yi facaka da kudin Amurkawa 'yan siyasa na kasar Amurka ne irinsa. Ya soki hukumar WHO, don neman karkatar da hankalin jama'ar kasar Amurka, gami da dora laifin tsanatar yanayin cutar a kasarsa ga saura. Abun da ya yi ya nuna yadda yake kyamar hukumomin kasa da kasa, gami da ka'idojin da ake bi a duniya, inda yake ta kokarin daukar matakai na kashin kai, bisa ra'ayi na yin babakere a duniya.

Hukumar WHO bisa matsayinta na hukumar da ta shafi bangarori daban daban, wadda ta fi taka muhimmiyar rawa a fannin aikin lafiya, tana ta kokarin sauke nauyinta, bayan barkewar cutar COVID-19. Bayan hukumar ta samu rahoton da kasar Sin ta mika mata a ranar 1 ga watan Janairu, nan take ta yi gargadi ga kasashe daban daban. Sa'an nan ta fara tura bayanai kan yadda ake fama da cutar ga jami'an lafiya na kasashen duniya a kai a kai, tun daga ranar 7 ga watan Janairu. Zuwa watan Fabrairu, hukumar ta aike da wata tawagar kwararru domin su yi ziyarar aiki a kasar Sin. Cikin kwararrun har da wasu jami'an lafiya 2 na kasar Amurka.

Duk da wadannan ayyukan da hukumar WHO ta yi, fadar shugabancin kasar Amurka White House, ba ta sanar da halin ta-baci a kasar Amurka ba, sai zuwa ranar 13 ga watan Maris, wato bayan kwanaki 40 da hukumar WHO ta yi gargadi ga dukkan kasashen duniya.

Kowa zai iya ganin gaskiyar hakan, don haka ba wani abu da mista Pompeo zai iya boyewa ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China