Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin gwiwa shi ne makami mafi karfi wajen yaki da cutar COVID-19
2020-04-28 15:04:50        cri
A kwanakin baya, tsohon firaministan kasar Faransa Jean-Pierre Raffarin, ya jinjinawa Sin bisa rawar da ta taka a yaki da cutar COVID-19, ya ce, a yayin da ake fuskantar cutar, Sin ta aiwatar da hadin gwiwa da kasa da kasa, tare da raba fasahohinta na yaki da cutar, hakan ya shaida yadda ta sauke nauyin ta a matsayin babbar kasa a duniya, don haka ya nuna girmamawa ga jama'ar kasar Sin.

A farkon shekarar bana, cutar COVID-19 ta abku ba zato ba tsammani, bisa jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping, jama'ar kasar Sin biliyan 1 da miliyan 400, sun yi kokari tare, da hadin gwiwa da juna, don kare yaduwar cutar, inda kuma suka samu gaggarumar nasara wajen yaki da cutar.

A yayin da ake aikin kandagarkin cutar a fadin duniya, ko kadan Sin ba ta janye jikinta ba. Bayan da cutar ta abku, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, makoma bai day ace ga dukkanin bil Adam, kuma hadin gwiwa shi ne makami mafi karfi wajen yaki da cutar.

Hakazalika kuma, Sin ta bi ka'idojin bayyana yanayin cutar ba tare da rufa rufa ba, da daukar alhakin da ke bisa wuyanta, inda ta sanar da yanayin cutar ga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO cikin lokaci, tare da gabatar da bayanai game da nazarin kwayoyin cutar ga dukkan duniya, ta kuma aiwatar da hadin gwiwa a tsakanin masanan kasa da kasa wajen yaki da cutar.

Tun daga watan Maris, cutar COVID-19 ta tsananta yaduwa a dukkan duniya, wadda ta shafa kasashe da yankuna fiye da 200, lamarin da ya haifar da babban kalubale ga ayyukan kiwon lafiya na duniya. Sin ta samar da gudummawa ga kasashen duniya wajen yaki da cutar bisa yanayin da ta samu na wasu nasarori a wannan fanni.

A halin yanzu, kasar Sin tana kokarin samar da kayayyakin yaki da cutar ba rana ba dare, don samar da gudummawa ga kasa da kasa wajen yaki da cutar.

Babu shakka, cutar ba ta san kasa ba, kuma ba ta san kabila ba, kuma hadin kan juna da taimakon juna hanya ce da ya kamata 'yan Adam su bi don shawo kan cutar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China