Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wace shaida wasu 'Yan Siyasar Amurka Ke Neman Boyewa?
2020-04-29 20:59:18        cri

Jaridar Los Angeles Times ta kasar Amurka ta ba da labari a kwanan baya cewa, bisa wani rahoton da aka gabatar game da binciken da aka yi kan gawarwakin mutanen da suka mutu sakamakon cutar COVID-19, an gano cewa daya daga cikinsu ya mutu ne a ranar 6 ga watan Fabrairun da ya gabata, wato makonni 3 kafin lokacin da hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka ta sanar da samun mutum na farko a kasar da ya mutu sakamakon COVID-19.

Ko da yake wasu 'yan siyasan kasar Amurka suna ta kokarin dora asalin cutar ga kasar Sin, amma binciken da aka yi ya nuna cewa, mutum na farko da ya mutu sakamakon COVID-19 a kasar Amurka bai taba ziyara zuwa wata kasa ba. Saboda haka, Jeff Smith, shugaban gundumar Santa Clara ta kasar Amurka, wanda ya ce ya yiwu an fara samun yaduwar cutar COVID-19 tsakanin al'ummar gundumarsa tun daga watan Disamban shekarar 2019.

Hakika karin shaidun da ake samu sun nuna cewa, cutar COVID-19 ta fara bullowa ne a kasar Amurka, kafin lokacin da hukumar kasar Amurka ta sanar da bullar cutar. Sai dai ko gwamnatin kasar ba ta san kome game da bullar cutar ba a karon farko? Sannan mutane nawa ne suka kamu da cutar a kasar? Ko kasar tana fakewa da wata mura don boye bullar cutar COVID-19? Sa'an nan me ya sa gwamnatin kasar Amurka ta kasa daukar managartan matakai wajen tinkarar cutar, amma ta dage wajen dora laifi ga 'yan kasar dake neman dakile cutar, gami da kasar ta Sin?

Duk wadannan tambayoyi na kara janyo hankalin Amurkawa, sai dai har yanzu gwamnatinsu ba ta ce komai ba, maimakon haka ma, tana ta kokarin dora wa kasar Sin laifi. Ko a idon wasu 'yan siyasar Amurka, rayukan jama'ar fararen hula ba su da daraja? Suna kare 'yancin bil Adama ne kamar haka? (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China