Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Annobar COVID-19 Ta Ba Duniya Damar Sanin Halayyar Sinawa
2020-04-29 20:02:48        cri

Babban mashawarci shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Mista Bruce Alyward, ya taba ziyartar kasar Sin a watan Fabrairun da ya gabata, sa'an nan ya bayyana wa manema labaru cewa, " Ko da yake babu kowa a titunan birnin Wuhan, amma a bayan kowace taga da mutum ya gani, to akwai mutanen birnin Wuhan dake martaba umarnin da aka bayar don tinkarar annobar. Yadda Sinawa suke zama tsintsiya madaukinki daya yana da burgewa matuka."

Hakika a wannan yakin da kasar Sin ta yi da mummunar cutar nan ta COVID-19, halayyar Sinawa da al'adun gargajiyar kasar na taka muhimmiyar rawa.

Daya daga cikin tunani da al'adun kasar Sin ya kunsa shi ne kokarin kula da jama'a. Wannan ra'ayi ya sa jami'an kasar sub a da matukar muhimmanci ga rayukan jama'a. Har ma shugaba Xi Jingping na kasar Sin shi ma ya sha nanatawa, cewar ya kamata a ba da muhimmanci ga batun tsaron lafiyar fararen hula.

Ban da haka, cikin dalilan da suka sa kasar Sin ta yi nasarar shawo kan yaduwar cutar COVID-19 cikin sauri, akwai ra'ayin kishin kasa da sadaukar da kai da Sinawa suka nuna.

Saboda kishin kasa ne, wasu jami'an lafiya fiye da dubu 42 suka tafi birnin Wuhan, inda yanayin yaduwar cutar COVID-19 ya fi kamari a lokacin, don ba da taimako wajen ceto rayukan mutane a can. Yayin da a nasu bangare, daukacin al'ummar kasar biliyan 1.4 sun amsa kiraye-kirayen da aka yi musu na zama a gida, don ba da tasu gudunmawa ga aikin dakile cutar COVID-19.

Haka zalika, yadda jama'ar kasar suke kokarin hana yaduwar cutar ya nuna ra'ayinsu na taimakawa juna. Ana iya ganin yadda al'ummar kasar suka yi ta tura kayayyaki da abinci da ake bukata zuwa birnin Wuhan, bayan fara daukar matakin killace birnin. Sa'an nan dukkan Sinawa, har ma da wadanda suke kasashen waje, sun ba da tallafi da yawa ga mutanen birnin Wuhan, tare da kokarin karfafa musu gwiwa.

Wadannan abubuwa sun nuna yadda Sinawa suke samun fifiko a fannin halayyarsu da al'adunsu masu daraja. Sa'an nan ta wannan fifiko sun samu kwarin gwiwa sosai kan makomar kasar Sin da al'ummarsu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China