Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu kamuwa da COVID-19 a Afrika sun kai 34,915 kana 1,521 sun rasu
2020-04-30 09:18:55        cri
Cibiyar yaki da yaduwar cututtuka ta Afrika wato Africa CDC ta ce, ya zuwa jiya Laraba adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 1,521, yayin da wadanda suka kamu da cutar sun karu zuwa 34,915.

Africa CDC, cibiyar kwararrun ta kungiyar AU mai mambobin kasashe 55, ta sanar a rahotonta na baya bayan nan a ranar Laraba cewa, adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 ya karu a nahiyar daga 31,933 a ranar Talata zuwa 34,915 a yammacin ranar Laraba.

Kawo yanzu cutar ta yadu a kasashen Afrika 52, a cewar sanarwar.

Africa CDC ta sanar cewa, kimanin mutane 11,309 sun warke daga cutar COVID-19 a nahiyar ya zuwa ranar Laraba, hakan ya nuna cewa, an samu sabbin mutane 1,157 da suka warke daga annobar sama da adadin mutane 10,152 da suka warke ya zuwa yammacin Talata.

A cewar cibiyar Afrika CDC, adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a fadin nahiyar ya karu daga 1,469 a yammacin Talata zuwa mutane 1,521 a yammacin Laraba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China