Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiya na kara inganta
2020-04-29 15:09:51        cri
Cutar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da bazuwa a nahiyar Afirka, inda kasar Sin ke kokarin samar mata da taimako ta hanyoyi daban-daban. Kasar Sin da kasashen Afirka suna da da makomar bil'adama ta bai daya, musamman tun barkewar cutar mashako ta COVID-19, hadin-gwiwar bangarorin biyu na kara inganta.

Tun farkon bullar cutar, kungiyar sada zumunta tsakanin Comoros da Sin ta baiwa gwamnatin kasar Sin kyautar kudin ERUO 100, duk da cewa kasar Comoros na fama da talauci. A yayin da al'ummar kasar Sin ke himmatuwa wajen yaki da cutar, kasashe gami da al'ummar Afirka sun samar mata da goyon-baya da taimako kwarai da gaske.

A kwanan nan, an shirya taron bidiyo ta kafar intanet tsakanin kwararrun likitoci da jami'an gwamnati tsakanin kasar Sin da na kasashen Afirka daban-daban, ciki har da Najeriya, da Kenya, da Masar, da Morocco, da Angola da sauransu, inda suka yi musanyar ra'ayoyi kan dabarun yaki da annobar. Kuma irin wadannan tarurruka ta kafar bidiyo, sun samu amincewa sosai daga kwararrun Afirka, inda suka jinjina manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin yaki da yaduwar cutar, da babbar gudummawar da ta bayar ga kare lafiyar al'umma a duk fadin duniya. Haka kuma kwararrun Afirka sun jaddada cewa, dabarun Sin abubuwan koyi ne, wadanda suka kafa misalai ga kasashen Afirka wajen dakile yaduwar cutar. Ban da shirya tarurrukan musanyar dabaru ta kafar bidiyo, kasar Sin ta kuma tura tawagogin ma'aikatan lafiyarta zuwa kasashen Afirka daban-daban don taimaka musu yaki da annobar.

Hakika, hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin lafiya na da dogon tarihi. Kawo yanzu, akwai ma'aikatan lafiyar kasar Sin sama da dubu 20 wadanda suka samar da taimakon jinya ga kasashen Afirka fiye da 50, musamman a fannin yaki da cututtuka masu yaduwa, ciki har da zazzabin cizon sauro, da kwalara da kuma cutar Ebola.

A hain yanzu ma'aikatan lafiyar kasar Sin kusan 1000 suna kasashen Afirka daban-daban, domin taimaka musu yaki da cutar numfashi ta COVID-19.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China