Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta fannin yaki da cutar COVID-19 ya karfafa
2020-04-18 16:15:23        cri

A baya bayan nan, Jami'an lafiya na kasar Sin sun isa kasashen Habasha da Burkina Faso. Lamarin da ya sa shugaban kasar Burkina Faso Roch Marc Christian KABORE ya bayyana ta kafar sada zumunta cewa, wasu ma'aikatan lafiya 12 na kasar Sin sun isa Ouagadougou, don taimakawa yaki da cutar COVID-19. Kuma suna musu maraba da zuwa, tare da gode musu.

 

 

A kwanan nan kuma, gudummawar kayayyakin kiwon lafiya da gwamnatin kasar Sin da kamfanonin kasar suka samar, suka isa kasashen Afirka, inda manyan jami'an kasashen da dama suka bayyana godiyarsu ga kasar Sin.

 

 

Sai kuma a jiya Juma'a, kwararrun masana sama da 60 da suka fito daga kasar Sin da ma kasashen Afirka 13, ciki har da Nijeriya da Afirka ta kudu da Masar da Kenya da Mali da Burkina Faso da Kamaru da sauransu, suka yi taron kara wa juna sani mai taken "inganta karfin tinkarar annoba domin makoma ta bai daya ta kasashen Sin da Afirka", inda suka yi musayar ra'ayoyi da kuma gabatar da shawarwari dangane da yadda sassan biyu za su hada gwiwa da nufin cimma nasara kan cutar.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China