Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagogin jamian lafiya da kayayyakin tallafi da kasar Sin ta tura, sun isa wasu kasashen Afirka
2020-04-17 11:37:27        cri

Tawagar jami'an lafiya na kasar Sin, sun isa filin jirgin saman birnin Addis Ababa dake Habasha a jiya Alhamis. Tawagar mai kunshe da mambobi 12 ita ce ta farko da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa nahiyar Afrika, inda za su kasance a kasar tsawon kwanaki 15.

Jirgin da ya kai tawagar na kuma dauke da kayayyakin kariya da sauran kayayyakin kiwon lafiya da magungunan gargajiya na kasar Sin, wadanda za su taimakawa kasar Habasha.

Baya ga wannan, bisa gayyatar gwamnatin Burkina Faso, tawagar jami'an lafiya na kasar Sin masu yaki da annobar COVID-19 sun isa Ouagadougou, babban birnin kasar a jiya Alhamis.

Kwararrun na kasar Sin na yayata gogewarsu ta fuskar yaki da annoba a asibitoci, da kai daukin gaggawa. Ko a ranar Litinin, sun horar da likitocin kasar Rwanda dake aikin yaki da annobar ta kafar yanar gizo ta Internet.

Bugu da kari, gudunmuwar kayayyakin kiwon lafiya na yaki da COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta bayar, sun isa birnin Brazzaville na Jamhuriyar Congo. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China