Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19 ta yi sanadin mutuwar mutane 1,080 a Afrika, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun harbu a nahiyar ya kai 21,317
2020-04-20 09:54:56        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Tarayyar Afrika wato Africa CDC, ta ce adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar annobar COVID-19 a nahiyar ya kai 1,080, yayin da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu ya kai 21,317, ya zuwa jiya Lahadi.

Cikin rahoton da ta fitar a jiyan, cibiyar Africa CDC ta kuma bayyana cewa, kawo yanzu, an samu bullar cutar a kasashen nahiyar 52, inda kuma ta fi kamari a kasashen Masar da Afrika ta Kudu da Algeria da kuma Morocco.

Yayin wani taron manema labarai ta kafar bidiyo a ranar Jumma'a, daraktan cibiyar John Nkengasong, ya bayyana muhimmancin dake tattare da karfafa daukar matakan kandagarki a fadin nahiyar domin dakile ci gaba da yaduwar cutar.

Ya kara da cewa, matakin takaita zirga-zirga da kasashen nahiyar suka dauka ka iya illa kan harkokin tattalin arziki da zamantakewa, amma alfanun da zai yi a nan gaba na da yawa. Yana mai cewa, zai ceci rayuka tare da taimakawa wajen gaggauta kawo karshen annobar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China