![]() |
|
2020-04-21 11:15:08 cri |
Hadaddiyar kungiyar kamfanoni masu zaman kansu a Najeriya ta sanar a ranar Litinin cewa, ta bayar da odar sayen kayayyakin gwaje gwaje 250,000 da kuma karin wasu kayan gwajin 150,000 domin gaggauta aikin gwajin annobar COVID-19 mai saurin kisa a kasar.
A sanarwar da ta aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kungiyar tace ta kafa wasu cibiyoyi biyar a jahohin Legas, Kano, Rivers, Borno da Enugu da kuma birnin tarayya Abuja, yayin da take cigaba da aikin gyare gyaren wasu asibitoci da kuma samar da magunguna a sauran jahohin kasar.
Kungiyar tace hakikanin halin da ake ciki a yanzu, dole ne a mayar da hankali tare da yin hadin gwiwa tare don cimma nasarar yaki da wannan annoba.
A cewar kungiyar magidanta a kalla miliyan 1.7 ne suka amfana da shirinta na bayar da tallafin abinci a matsayin wani bangare na rage radadin dokar zaman gida da gwamnatoci suka kafa a wasu biranen kasar.
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China