![]() |
|
2020-02-23 16:13:32 cri |
Zong Changqing ya ce, saboda lokacin barkewar cutar ya yi karo da lokacin hutu na bikin sabuwar shekarar kasar Sin, kamfanoni masu jarin Sin da na waje na cikin mawuyacin hali, alal misali, ma'aikata ba su iya komawa bakin aiki cikin lokaci ba, da hana zirga-zirga a kasar, da karancin kayayyakin kandagarki da rashin samun kayayyaki da dai sauransu, dukkan matakan sun sanya yawancin kamfanoni na fuskantar matsalar farfado da aikinsu. A wani bangare kuwa, barkewar cutar ta baiwa masu zuba jari damuwa sosai, har suna sa ido kan lamarin. A watan Janairun bana, yawan jarin wajen da aka yi amfani da shi ya yi daidai da na makamatan lokacin bara, amma saurin karuwar adadin ya dan koma baya.
An kiyasta cewa, ya zuwa karshen watan Fabrairu, yawancin wurare za su dawo bakin aikinsu. Ban da wanann kuma, Sin za ta dauki matakai da suka dace don habaka sana'o'i da za su shigo da jarin waje, don kara kyautata yanayin zuba jari a kasar. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China