![]() |
|
2020-04-18 16:34:43 cri |
Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun Xinhua, babban jami'in kula da ayyuka na kamfanin Boye Olusanya, ya ce a matsayinsa na babban kamfani mai hannu jari a Nijeriya, kuma wanda ke bada gagagrumar gudunmuwa ga yunkurin kasar na ciyar da al'ummarta, Flour Mills, ya sayi kayayyakin kiwon lafiya da darajarsu ta kai kimanin dala miliyan 1.5, wadanda za su gaggauta karfafa karfin kasar na gwajin cutar COVID-19.
Ana sa ran kayayyakin wadanda za a kai cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta kasar wato NCDC, za su isa kasar kafin ranar 27 ga watan Afrilu, daga kasashen da suka hada da Amurka da Canada da Sin. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China