Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a goyi bayan WHO ta fuskar jagorantar harkokin kiwon lafiyar gaggawa na kasa da kasa
2020-04-20 10:51:23        cri
Shugaban kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin, Ma Xiaowei, ya yi kira ga kungiyar G20, ta ci gaba da goyon bayan hukumar lafiya ta duniya WHO, wajen jagorantar harkokin kiwon lafiya na gaggawa da suka auku cikin kasa da kasa.

Ma Xiaowei ya yi kiran ne a jiya Lahadi da dare, yayin taron bidiyo na ministocin lafiya na kasashen kungiyar G20.

Ya kara da cewa, bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin ta samar da bayanai ga hukumar WHO da gamayyar kasa da kasa a kan lokaci, kuma ba tare da boye kome ba, sannan ta sauke nauyinta yadda ya kamata. Ya ce a nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da sabunta labarai a shafin intanet na cibiyar goyon bayan aikin kandagarki da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, game da yadda za a yi kandagarkin cutar da jinyar wadanda suka kamu, da kuma taimakawa kasashen dake bukata.

A nasa bangaren, babban darektan hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, yana farin ciki sosai da ganin mambobin kungiyar G20 za su soke matakan killace birane, amma abu mafi muhimmanci shi ne, ya kamata a aiwatar da matakan bi da bi. Ya ce, soke matakan killace birane ba ya nufin an kawo karshen yaduwar annobar a wata kasa, sai dai, farawa da wani sabon mataki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China