Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya ya karu zuwa 288
2020-04-10 19:38:29        cri
Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana yayin rahoton rana-rana da take bayarwa game da yanayin cutar a kasar jiya Alhamis cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ya karu zuwa 288.

Cibiyar ta ce, an samu karin mutane 14, kan 276 da ake da shi a baya, an kuma sallami mutane 51 bayan da suka warke daga cutar, akwai kuma mutane 7 da cutar ta halaka ya zuwa yanzu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China