Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi: Sin ta jaddada kawancenta da Serbia ta hanyar tallafawa yaki da cutar COVID-19
2020-04-15 13:09:44        cri

A jiya Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada dankon zumuntar dake tsakanin kasar sa da Serbia, yana mai cewa tallafin da Sin ta samar ga Serbia, a gabar da kasar ke fama da kalubalen cutar numfashi ta COVID-19, ya sake alamta darajar kawancen sassan biyu.

Shugaban na Sin ya yi wannan tsokaci ne, yayin zantawar sa ta wayar tarho da takwaransa na Serbia Aleksandar Vucic. Ya ce Sin ta samarwa Serbia tallafin kayan kula da lafiya na gaggawa da take bukata, tare da sauran kayayyakin kare kai, ta kuma tura kwararrun masana a fannin kiwon lafiya zuwa kasar dake nahiyar Turai, za ta kuma ci gaba da ba taimako da goyon baya ga Serbia, a yakin da take yi da cutar COVID0-19.

A nasa tsokaci yayin tattaunawar, Mr. Vucic ya ce yana matukar farin cikin ganin yadda Sin ta kai ga shawo kan cutar COVID-19 a cikin gida. A hannu guda kuma Sin ta karfafa gwiwar al'ummar Serbia, a kokarin da suma suke yi na ganin bayan wannan annoba.

Kaza lika ya jaddada cewa, duk tsanani da yawan kalubale da za a iya fuskanta, al'ummar kasar sa za su ci gaba da zama abokai na gari ga Sinawa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China