2020-04-15 21:39:11 cri |
Bayanin ya jaddada cewa, makomar 'yan Adam daya ce. Hadin kan kasa da kasa shi ne makami mafi karfi wajen yakar cutar COVID-19 da take barazana ga lafiyar al'ummar kasa da kasa. A yayin da cutar COVID-19 ke yaduwa a fadin duniya, akwai bukatar kasashen duniya su karfafa niyyarsu da hada kai, ta yadda za su samu galaba kan wannan yakin da 'yan Adam ke yi da mummunar cutar. Bayanin ya kara da cewa, idan har muka hada kai tare da taimakon juna, tabbas za mu yi nasara kan wanan cuta, ta yadda gobe za ta yi kyau ga ci gaban bil-Adama.(Lubabatu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China