Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a kara inganta manyan manufofin gwamnati domin rage illar da cutar COVID-19 ke haifarwa
2020-04-17 21:05:52        cri
Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya shugabanci taron ofishin siyasa na kwamitin. Taron ya jaddada cewa, ya zama dole a kara farfado da ayyuka a bangarori daban-daban a yayin da kasar ke ci gaba da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da maido da tsare-tsaren tattalin arziki da zaman rayuwar al'umma yadda ya kamata, tare kuma da lalibo sabbin hanyoyin raya tattalin arzikin kasar.

A dayan bangaren, taron ya sake jaddada muhimmancin fadada hadin-gwiwa tsakanin kasa da kasa wajen dakile annobar, da zurfafa mu'amala da hadin-gwiwa tsakanin Sin da hukumar WHO, da ci gaba da samar da agaji ga kasashen da suke da bukata, da ba da gudummawa ga hadin gwiwar kasashen duniya na yakar annobar a fannoni daban-daban.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China