![]() |
|
2020-04-17 10:53:33 cri |
A ranar 16 ga watan Afrilun 2020, gwamnatin Sin ta aike da tallafin kayayyakin kiwon lafiya karo na biyu ga Najeriya domin yaki da annobar COVID-19. Li Yuan, jami'in sashen kasuwanci a ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya, ya halarci bikin mika tallafin kayayyakin a filin jirgin saman Abuja tare da babban daraktan sashen hadin gwiwar kasa da kasa na ma'aikatar kudin Najeriya.
Li ya fada cikin jawabinsa cewa kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Najeriya domin kawo karshen wahalhalun da kasar ke fuskanta wajen yaki da annobar. A madadin gwamnatin Najeriya, Yakubu, ya godewa gwamnatin kasar Sin saboda samar da tallafin kayayyakin kiwon lafiyar, ya ce ya yi amanna bisa ga hadin gwiwar kasashen biyu, Najeriya za ta samu nasarar kawo karshen annobar COVID-19.
Bugu da kari, kashin farko na tallafin kayayyakin kiwon lafiyar da gwamnatin kasar Sin ta baiwa Najeriya don yaki da annobar COVID-19 ya isa birnin Legas a ranar 13 ga watan Afrilu. Kayayyakin tallafin lafiyar na gaggawa karo biyu sun hada da rigunan bada kariya ga jami'an lafiya, da takunkumin rufe baki da hanci samfurin KN95, da takunkumin rufe baki da hanci wanda jami'an lafiya ke amfani da shi, da safar hannu, da abin rufe takalma da kuma na'urar gwajin yanayi. (Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China