Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Kamata ya yi a ingiza dangantakar Afrika da Sin a dogon lokaci bisa cikakken sanin ya kamata
2020-04-17 10:59:36        cri

A jiya Alhamis ne babban editan jaridar "This Day" ta Najeriya Olusegun Adeniyi, ya rubuta wani bayani a jaridar mai taken "Sin, COVID 19 da fushin Afrika", inda ya bayyana cewa, ya kamata a bunkasa dangantaka da zumunci dake tsakanin Afrika da Sin, musamman ma a halin yanzu da wannan mummunar cuta ta COVID-19 ke dabaiye duk fadin duniya, take kuma babbar illa ga bangarorin biyu, don haka kamata ya yi a kara fahimta, da amincewa da juna, da kuma kara hadin kai tsakanin sassan biyu.

Kaza lika ya yi tir da wasu mutane, wadanda suke baza jita-jita, da kuma matakan da wasu mutanen dake kan mukamai masu muhimmanci suke dauka, yana mai kira ga bangarorin biyu, da su kara tuntubar juna, da magance matsalolin da suke bullowa, bisa ra'ayin cikakken sanin ya kamata, ta yadda za a murkushe duk wani yunkuri na illata dangantakar bangarorin biyu.

Bayanin ya ce, Sin ta samu nasarar dakile cutar COVID-19 bisa matakai-matakai, saboda ganin tsauraran matakai da take dauka a dukkanin fannoni masu amfani, kana kamata ya yi kasa da kasa su yi koyi daga kasar Sin a wannan fanni.

Ya ce idan Najeriya tana son dakile wannan cuta, kamata ya yi ta kara hadin kai da kasar ba tare da bata lokaci ba, amma shafawa kasar Sin bakin fenti a wannan muhimmin lokaci na da wata manufa ce ta daban. Ya ce, ya kamata Afrika ciki hadda Najeriya da kuma kasar Sin, su koyi darasi daga yadda ake tinkarar jita-jita, don sa kaimi ga raya dangantakar bangarorin biyu yadda ya kamata a dogon lokaci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China