Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cutar COVID-19 ta yi sanadin mutuwar babban hadimin shugaban Nijeriya
2020-04-18 16:28:13        cri

Allah ya yi wa Mallam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, rasuwa bayan ya kamu da cutar COVID-19.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce Mallam Abba Kyari da ya dara shekaru 70, wanda kuma ke da wasu matsalolin lafiya na daban, ya rasu ne a jiya Jumma'a. kuma ya kasance daya daga cikin makusantan shugaba Buhari.

Marigayin ya kamu da cutar COVID-19 ne bayan ya koma gida daga kasar Jamus a cikin watan Maris.

A ranar 29 ga watan Maris ne ya tabbatar cikin wata sanarwa cewa, yana kan hanyarsa ta zuwa asibiti a jihar Lagos, cibiyar kasuwanci ta kasar, domin jinya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China