Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bada gudunmuwar kudi da kayayyakin lafiya domin taimakawa Nijeriya yaki da cutar COVID-19
2020-04-18 16:23:11        cri

Kasar Sin ta mika sama da dala 91,000 da kayayyakin kariya da na kiwon lafiya ga gwamnatin jihar Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriya, da nufin taimaka mata yaki da cutar COVID-19.

Karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake jihar Lagos da hadin gwiwar kungiyar Sinawa mazauna kasashen waje reshen Nijeriya ne suka bada gudunmuwar kayayyakin da suka hada da; marufin baki da hanci 12,000 da rigunan kariya na ma'aikatan lafiya guda 100 da ma'aunin yanayin zafin jiki 2,000 da safar hannu 2,000 da sinadarin tsaftace hannu 1,550 da injin taimakon numfashi guda daya.

An mika chekin kudin ne da kayayyakin ga kwamishinan sufuri na jihar, Fedrick Oladehinde.

A jawabinta na mika gudunmuwar, shugabar kungiyar Sinawa mata ta Nijeriya, Zhou Jun, ta ce annobar COVID-19 ta zama babban kalubale ga duniya, kuma gwamnati da al'ummar kasar Sin za su ci gaba da goyon baya tare da aiki da Nijeriya da ma jihar Lagos wajen yaki da cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China