![]() |
|
2020-04-16 11:18:47 cri |
A jiya ne, jaridar "The Nation" da ake wallafawa a tarayyar Najeriya, ta rubuta wani bayani mai taken "nuna shakka ga kasar Sin", inda a cikin sa ta yabawa kasar Sin, bisa zama a kan gaba, game da yakin da ake yi da cutar COVID-19 a duniya, da samun fasahohi da dama a wannan fanni, da kawo tasiri ga sauran sassan duniya.
Jaridar ta kuma jaddada cewa, goyon baya, da taimako da kasar Sin ta samar za su inganta karfin Nijeriya na yaki da cutar COVID-19, kuma zargin da ake yiwa kasar Sin ba shi da wani tushe.
Bayanin ya kara da cewa, yanzu haka ana samun yaduwar cutar COVID-19 a duniya cikin sauri, kuma babu wata kasa za ta iya tinkarar wannan cuta ita kadai, Najeriya ita ma haka take.
A kwanakin baya, tawagar aikin kandagarkin cutar ta kamfanin CRCC na kasar Sin, da kayayyakin aikin likitanci da nauyin su ya kai ton 16, sun isa Najeriya, hakan ya inganta karfin kasar wajen tinkarar cutar. Kuma ko da yake yawan 'yan Najeriya da suka kamu da cutar, da kuma wadanda suka mutu a sakamakon cutar ba su da yawa, amma a hannu guda, ba a san cikakken yanayin kamuwar cutar a dukkan kasar ba, don haka bai kamata a nuna shakka, ko kin amincewa da gudummawar kasar Sin ba, abun da ya wajaba shi ne hana yaduwar cutar. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China