Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Najeriya ya yi karin haske kan batun birnin Guangzhou
2020-04-15 16:32:53        cri

Jiya Talata agogon Najeriya, jakadan Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya kira wani taron manema labarai, bayan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama. Yayin taron, ministan ya yi karin haske game da zargin wai an ci zarafin 'yan Najeriya a birnin Guangzhou, inda ya yi bayani kan lamarin, sannan kuma ya gabatar da halin da 'yan kasar ke ciki a birnin Guangzhou wadanda aka killace su.

Onyeama ya ce, an tabbatar wasu 'yan kasar sun kamu da cutar COVID-19 lokacin da suka isa birnin Guangzhou. Daga baya kuma an tabbatar da cewa, wata mata basinniya mai dakin cin abinci ta kamu da cutar, wannan dakin cin abinci kuwa wuri ne da 'yan Afrika ciki hadda 'yan Najeriya suke taruwa domin cin abinci, saboda haka, gwamnatin birnin ta sanar da rufe wannan wuri, tare da killace wadanda suka yi mu'ammala da wannan mata, hakan ya sa duk mutanen da aka killace, ba shakka ba za su iya komawa otel, ko wuraren da suka taba zama ba.

Wasu 'yan Najeriya dake cikin kasar sun kalli bidiyon da ya shafi lamarin da aka yada shi a shfin sada zumunta na Intanet, sa'an nan sun yi gurguwar fahimtar cewa, wai ana nuna bambanci ga 'yan Najeriya, da ma sauran 'yan Afrika a birnin Guangzhou, yayin da ake tsaka da yaki da cutar, har kuma suka nuna rashin amincewa da hakan.

Onyeama ya kara da cewa, gwamnatin Guangzhou da ofishin karamin jakadan Najeriya dake birnin, sun kafa wani tsarin tuntubar juna mai amfani, suna hadin kai don bayyanawa 'yan Najeriya halin da ake ciki, ta yadda za su fahimci matakan da ake dauka a Guangzhou, na tabbatar da kare lafiya, da tsaron 'yan Afrika dake birnin.

Ban da wannan kuma, Onyeama ya nuna cewa, har illa yau an ba da kulawa ga 'yan Najeriya wadanda aka killace su a Guangzhou yadda ya kamata.

A nasa bangare, jakada Zhou Pingjian ya ce, ya zuwa ran 13 ga wata, yawan mutanen da aka tabbatar da shiga da kwayar cuta daga ketare ya kai 119, daga cikinsu 26 'yan kasashen waje ne, kuma 19 daga cikinsu 'yan Afrika ne, a ciki hadda 'yan Najeriya 9.

Ban da wannan kuma, yawan 'yan ketare dake dauke da cuta ba tare da nuna alama ba ya kai mutum 60, daga cikinsu 57 ne 'yan Afrika. Saboda ganin haka, 'yan Najeriya da ma sauran 'yan Afrika mazauna birnin na fuskantar babban hadari wajen lafiyar jiki da tsaro idan sun yi mu'ammala da wadanda suka kamu da cutar, abin da ya sa ake mai da hankali sosai wajen bincike, da kuma gwada kwayar cutar a jikinsu, don tabbatar da lafiyar jikinsu, da na sauran mazauna birnin.

An yi hakan ne domin dakile yarduwar cutar COVID-19, ba shi da alaka da nuna wariya da bambanci. A hakika ma dai, birnin Guangzhou na yin bincike kan dukkan wadanda ke cikin babban hadarin kamuwa da cutar, kuma yawan mutanen da aka killace su a wurare da aka tanada, ko a gidajensu yanzu haka ya kai dubu 15, daga cikinsu yawan 'yan ketare ya kai 4600. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China