![]() |
|
2020-04-15 11:11:47 cri |
Jiya Talata, Jaridar "Daily Sun" ta Najeriya, ta wallafa wani sharhi mai taken "Babu ma'ana ko kadan da a zargi likitocin kasar Sin dake tallafawa Najeriya", inda ta nanata cewa, an riga na tabbatar da cewa, fasahohi da kuma dabarun kasar Sin na yakar COVID-19 na da amfani matuka, don haka tawagar yakar cuta da CRCC ta tura zuwa Najeriya, za ta baiwa kasar tallafi mai inganci. Sabo da haka jaridar ta yi kira ga likitocin Najeriya, da su kara inganta mu'ammalar su, a kokarin ganin bayan cutar cikin hanzari.
Sharhin ya ce, tawagar kamfanin CRCC za ta hada kai da likitocin Najeriya, wajen yin musanyar ra'ayi kan fasahohi, da dabaru na yaki da cutar, amma ba za su yi aikin ba da jiyya kai tsaye a kasar ba.
A sa'i daya kuma, an kawo kayayyaki, da kuma na'urorin jiyya da Najeriya ke matukar bukata, har ila yau mambobin tawagar za su ba da jagoranci, kan yadda za a yi amfani da wadannan kayayyaki.
Najeriya ba ita kadai ce ke neman taimako daga kasar Sin ba, ganin yadda birnin New York na Amurka ma ya gayyaci ma'aikatan jiyya na kasar Sin domin su ba da taimako a Amurka. Don haka an iya ganin cewa, hadin kai da kasar Sin wajen tinkarar cutar COVID-19 wani mataki ne mai dacewa matuka.
Sharhin ya kuma ce, an gano matsaloli da dama cikin tsarin ba da jiyya na Najeriya a lokacin da ake tsaka da yaki da wannan cuta, don haka ya kamata a daina siyasantar da batun yaki da cutar, kuma a dora muhimmanci kan aikin rigakafa da dakile yaduwar cutar. Ya kara da cewa, taimakon da Sin take bayarwa a wannan lokaci na da ma'ana sosai, ya kuma burge Najeriya matuka. Kamata ya yi a yi amfani da wannan zarafi mai kyau, wajen hadin kai da tawagar CRCC, domin yakar wannan mumunar cuta tare. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China