Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen duniya na goyon bayan gudunmawar da WHO ke bayarwa wajen yakar COVID-19
2020-04-17 15:27:13        cri

Kwanan baya, gwamnatin Amurka ta sanar da dakatar da tallafinta ga hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO, abin da ya girgiza kasashen duniya gaba daya.

Gwamnatin Afrika ta kudu ta sanar a jiya cewa, ana matukar bukatar hadin kan duniya a wannan muhimmin lokaci. Kuma matakin da Amurka ke dauka zai illata kokarin da kasa da kasa suke yin na yakar cutar. Afrika ta kudu ta ce tana fatan Amurka ta sake nazarin halin da ake ciki don hadin kai da al'ummar duniya.

Jiya Alhamis kuma, Donald Trump shugaban Amurka ya jagoranci taron G7 ta bidiyo, inda ya ce, WHO ba ta ba da bayanai a bayyane kuma ta dauki matakan da ba su dace ba, inda ya yi kira da a yi bincike da gyaran fuska kan hukumar, amma ya kasa samun amsa daga sauran kasashe. Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Dorothea Merkel da kuma firaministan kasar Canada Justin Trudeau da dai sauran shugabanni dukkansu sun bayyana goyon bayansu ga gudunmmawar da WHO ke bayarwa wajen yakar cutar a duniya, tare kuma da yin kira ga al'ummar duniya da su dauki matakai masu inganci dake daidaita bangarori daban-daban don dakile cutar cikin hadin kai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China