Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: An tabbatar da mutane miliyan 1.21 sun kamu da cutar COVID-19 a duniya
2020-04-07 12:32:22        cri

Bisa kididdigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi, ya zuwa daren ranar 6 ga wata, gaba daya akwai mutane 1214973 da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 cikin kasashen duniya, yayin da mutane 67841 suka rasu sanadiyyar cutar. Kuma adadin mutanen da suka kamu da cutar a wajen kasar Sin ya kai sama da miliyan 1.13.

Kana, bisa sabon rahoto game da cutar numfashi ta COVID-19 na rana-rana da WHO ta fidda a jiya Litinin, ya zuwa karfe 10 na ranar 6 ga wata,agogon tsakiyar Turai, akwai karin mutane 77200 da suka kamu da cutar a duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China