Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Antonio Guterres ya jinjinawa WHO game da yaki da COVID-19 a Afirka
2020-04-16 09:55:54        cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya jinjinawa kwazon da hukumar lafiya ta duniya WHO ke yi, na yaki da cutar numfashi ta COVID-19 a sassan nahiyar Afirka.

Ya ce hukumar WHO tana ci gaba da tallafawa gwamnatoci, da dabarun gano masu dauke da cutar cikin hanzari. Kaza lika a farko farkon bullar cutar, kasashe biyu ne kacal ke da cibiyar gwajin kwayar cutar ta COVID-19 a Afirka, amma da tallafin WHO, a yanzu haka yawan kasashen nahiyar dake da irin wadannan cibiyoyi sun kai 47.

Yayin wani taro ta bidiyo a jiya Laraba, da daya daga kungiyoyi 5 na MDDr masu ruwa da tsaki a wannan aiki, wadda kuma ke da mambobi daga kasashen Afirka 54, Mr. Guterres ya ce WHO tana kuma samar da taimakon bayanai ga hukumomin lafiyar kasashen nahiyar nahiyar, baya ga tallafin da take baiwa kananan yankuna, na tabbatar da an wayar da kan al'umma yadda ya kamata.

Ya ce wannan annoba na da tasiri mai fadin gaske, kuma MDD da kungiyar tarayyar Afirka ta AU na aiki tare, wajen shawo kan tarin kalubale, da abubuwa masu jawo hankali da dama, dake da nasaba da yaki da cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China