Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakatar da biyan kudin mamba da Amurka ta yi ya fusata WHO
2020-04-16 10:02:32        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a jiya Laraba cewa, dakatar da biyan kudin mamba da kasar Amurka ta yi ga hukumar ya fusata WHO. Ya ce, hukumar WHO za ta yi hadin gwiwa da abokan hadin gwiwarta wajen tattara kudade, domin cika alkawarin da ta yi ta fuskar kiwon lafiya, da kimiyya da fasaha, ta yadda za ta ci gaba da bautawa al'ummomin kasa da kasa yadda ya kamata.

A taron manema labaran da aka gudanar a wannan rana a birnin Geneva, Mr. Ghebreyesus ya bayyana cewa, aiki da kuma nauyin hukumar shi ne nuna adalci ga kasashen duniya, kuma komai yawan al'umma, ko karfin tattalin arzikin su. Cutar numfashi ta COVID-19 tana iya yaduwa cikin kasashe, ba tare da bambance girman wata kasa, ko kankantar ta, ko kabilu daban daban da sauran su ba. Ya ce hukumar WHO ita ma a nata bangare ba ta son nuna bambanci. Don haka a yanzu, ya dace a yi hadin gwiwa domin fuskantar wannan abokiyar gaba ta dukkanin bil Adama.

Ya ce hujjar da shugaban kasar Amurka ya gabatar, ta dakatar da biyan kudin mamba ga hukumar WHO, ita ce wai hukumar WHOn ba ta gudanar da ayyukan yaki da annobar yadda ya kamata, shi ya sa a matsayin babbar kasa dake samar da kudade ga hukumar WHO, kasar Amurka ta yanke hukuncin janye tallafin ta ga hukumar.

A nasa bangare kuma, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a jiya cewa, idan har kasar Amurka ta na son yanke hukunci kan hukumar, akwai tsarin doka da za ta iya bi, kuma za a iya gudanar da wannan aiki a lokaci mafi dacewa, amma, aikin dake gaban mu a halin yanzu, shi ne kandagarki, da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China