Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya bukaci a taimakawa WHO bayan barazanar Trump na katse kudaden da Amurka ke baiwa hukumar
2020-04-09 10:32:09        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a taimakawa hukumar lafiya ta duniya WHO a takaice, bayan da Shugaba Donald Trump na Amurka, ya yi barazanar dakatar da kudaden da kasarsa ke baiwa hukumar.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya rabawa manema labarai, Guterres ya ce, ya yi imanin cewa, wajibi ne a tallafawa WHO, saboda muhimmancin kokarin da duniya ke yi na ganin bayan cutar numfashi ta COVID-19.

Jami'in na MDD ya ce, ba mu taba ganin irin wannan cuta a rayuwarmu ba, don haka tana bukatar daukar matakai. Hakika a irin wannan yanayi, akwai yiwuwar wasu bangarori na yiwa irin wannan batu bahaguwar fassara, kamar yadda Trump ya soki WHO.

A ranar Talata ne dai, Trump ta soki matakan da WHO ta ke dauka kan yaki da COVID-19, inda ya yi barazanar dakatar da kudaden da Amurkar take baiwa hukumar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China